Jarumar Kannywood Fatí Baffah Bararóji Kano Ta Bayyana Cútar Daké Damúnta Karara Ga Dunìya.
Gaskiyar ramewar Jaruma fati baffa bararoji…
Tun a safiyar jiya Asabar aka fara yaɗa waɗansu hotuna a soshiyal midiya na jarumar Kannywood Fati Baffa Fagge (Bararoji) waɗanda su ka nuna Fatin ta yi wata irin ramewa.
Fati ta amsa da cewa: “Gaskiya na yi mamaki da na ji mutane su na ta surutu a kan wannan hotunan, har ma ake cewa ba ni da lafiya. To ni lafiya ta ƙalau, ban yi rashin lafiya ba.
Bararoji: “Kawai dai gajiyar tafiya ce”
Abin dai da na sani cikin satin nan na yi tafiya zuwa Abuja, daga nan sai na wuce Sokoto wajen taron biki, kuma ban huta ba na dawo Kano. To wannan yanayi na tafiyar ya sa ni gajiya, duk ido na su ka faɗa, kuma na zo na yi hotunan a haka, shi ya sa ake ganin kamar ba ni da lafiya ko na yi wata rashin lafiya.
“To gaskiya lafiya ta ƙalau, kawai dai gajiyar tafiya ce.”
Tags:
Kannywood