Yadda Asirin wani mutum mai shekaru 40 ya tonu bayan yayiwa yarinya yar fyade.
Siyama ta rasu ranar Alhamis 29-09- 2022 kimanin karfe 4 na yamma a dalilin Fyade da wanda ake tuhuma wani Idi (Baba Idi) mai shekaru kimanin 40 zuwa sama, dake Zaune a Lungun Alhaji Halliru a unguwar Gama, karamar hukumar Nassarawa ya yi mata ranar Talatar da ta gabata.
Kimanin kwana shida da ya gabata, Idi ya dauki Siyama zuwa dakinshi ya bata alewa inda ya yi lalata da ita kuma ya tsoratar da ita cewa in dai ta fadawa Abbanta sai ya kasheta da Almakashi kuma ya hadata da magen gidansu ta cinyeta (kasancewar ta mai tsoron mage) ta kwatanta mana yadda ya dora mata almakashi a wuya yace sai ya yankata da shi idan ta fadawa Abbanta.
Bayan ta shigo gida an cire mata kaya za ayi mata wanka aka ga jini yana fitowa daga jikinta, aka ce me ya sameta tace “Baba Idi ne yake mun wani abu yauma ya ciremin wando ya yi min ya bani alawa kuma yace idan na fadawa Abbana ze kasheni, Umma don Allah kar ki fadawa Abba”. Daga nan aka dauketa aka kaita asibiti inda likitoci suka tabbatar da ‘Penetration’ kuma suka fadi hanyoyin da za a bi a kula da lafiyarta.
Bayan jami’an tsaro sun kamashi an kaishi CID ana cikin bada statement aka fito dashi da ankwa, tana ganinshi ta rude da firgici tana cewa “Umma yace kasheni zai yi da Almakashi, me yasa ki ka fadawa Abba? Kasheni ze yi kuma ze hadani da mage” daga nan zazzabi ya kamata aka dawo da ita gida, har zuwa washe gari da ta rasu tana ta maimaita kasheni zeyi da Almakashi.
Yau kwanan Siyama uku da rasuwa sakamakon Zalunci da cin zarafin da wannan la’anannen Allah ya yi mata, Allah ya gafarta mata yasa mai ceton iyaye ce shi kuma Allah ya kare Al’umma da sharrin mutane irinsa yasa ya girbi abinda ya shuka...
Wani magidanci mai shekaru 49, mai suna Baba Idi, ya shiga hannun ƴan sanda a Kano bisa zargin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 3 fyade, Khadija Adamu, wacce a ka fi sani da Yasmin.
An kama Bana Idi ne a ranar 29 ga watan Agustan 2022 biyo bayan mahaifin marigayiya Yasmin ya ƙorafi wajen ƴan sanda.
A wata hira da ya yi da SAHELIAN TIMES, kawun marigayiyar, Bilyamu Abubkar, ya bayyana cewa mahaifiyarta ta zo yi mata wanka, sai ta ga jini a al’aurar ta.
“Lokacin da mahaifiyarta ta tambaya, Yasmin ta tabbatar da cewa Baba Idi ne yake yi mata wani abu, kuma ya yi mata barazanar cewa zai kashe ta idan ta gaya wa mahaifinta,” in ji shi.
A baya dai baba idi ya taɓa shigar da marigayiyyar zuwa wani shagon gidansu yarinyar kuma ya yi mata fyade.
SAHELIAN TIMES ta ce ta samu kwafin rahoton likita, wanda ya tabbatar da an yiwa Yasmin fyade.
A cewar kawun, daga baya aka kai Yasmin shelkwatar ƴan sanda domin tantance wanda ake zargin.
Ya kara da cewa “Lokacin da ta gan shi, sai ta fashe da kuka, tana mai cewa ya yi alkawarin zai kashe ta kuma ya baiwa mage ta cinyeta,” in ji shi.
"Tun da ga nan Yasmin ta fara rashin lafiya, kuma banta jima ba bayan kwana uku ta rasu ta na ta nanata cewa “shi ne wanda ya ce zai kashe ni,"