Kwalliyar Da Yar Sarkin Kano Tayi A Ranar Bikin Ta Ya Jawo Cecekuce.


A ranar Juma’a 2 ga watan Satumba ne aka daura auren diyar sarkin Kano, Ruqayya Aminu Bayero da angonta dan sarkin Kibiya, Amir Kibiya.

Tun a karshen makon jiya ne aka fara shagulgulan bikin inda aka gudanar da bukukuwan al’ada irin su Lugude, kunshi, Gada da sauransu.

A yayin da ake shirin rufe bikin, an gudanar da wani hadadden liyafar dina a daren yau Asabar, 3 ga watan Satumba.

Amarya ta yi kasaitaccen shiga da ado na kece raini inda ta sanya wata hadaddiyar doguwar riga da aka yiwa ado da duwatsu masu walwali sannan daga baya an yi masa wani rufi irin na ‘ya’yan sarauta.

A daya daga cikin bidiyoyin shagalin da suka yadu a shafukan soshiyal midiya, an gano lokacin da amarya da ango da kuma wani dan uwansu suka shigo dakin taron cike da kasaita da kwarjini irin na jinin sarauta.

A baya mun ji cewa kwaryar birinin Kano ta cika ta batse a ranar Juma’a yayin da ‘dan sarkin Kibiya, Alhaji Umar Usman ya auri diyar Sarkin Kano, Rukayya Aminu Bayero inda manyan mutane suka halarci daurin auren.

Jim kadan bayan addu’o’in, Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda ya tsaya matsayin waliyyin amarya, yayi addu’ar Allah ya albarkaci auren tare da basu yara nagari.

An daura auren a fadar Sarkin Kano tare da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje wanda ya bayar da auren kan sadaki N200,000.

Post a Comment

Previous Post Next Post