Yan Sanda Sunyi Babban Kamu Sun Kama Ɓarayin Ragon Sallah


Yan sanda a jihar Ogun sun tsare wasu mutane biyu kan zarginsu da satar ragon babban sallah, Leadership ta rahoto.

 Eid el Kabir, da aka fi kira da babban sallah a Najeriya zai fado ne a ranar Asabar 9 ga watan Yulin 2022. 

 Yan sanda a jihar Ogun sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da aikata laifin satar ragon sallah Abimbola Oyeyemi.

 kakakin yan sandan ne ya sanar da hakan yana mai cewa wadanda ake zargin sun tafi da mota ne suka so sace ragon.

Waƴan da aka kama sune Adetunji Alagbe da Opeyemi Ogunlokun za su cigaba da zama hannun yan sanda yayin da ake zurfafa bincike kafin a kai su kotu.

 Kakakin yan sandan jihar Abimbola Oyeyemi, ya ce an kama wadanda ake zargin na Adetunji Alagbe da Opeyemi Ogunlokun, kan satar ragon wani Sodiq Abolere a Ogijo a Ikorodu Legas. 

Sanarwar ta ce: "Yan sanan Jihar Ogun a ranar 5 ga watan Yulin 2022, sun kama Adetunji da Opeyemi Ogunlokun saboda satar ragon sallah mallakar wani Sodiq Abolere.

 "An kama wadanda ake zargin ne bayan rahoton da wani Sodiq Abolore ya shigar d hedkwatar yan sanda ta Ogijo wanda ya ce misalin karfe 3 na dare yana barci a gidansa ya ji motsa da bai saba ji ba hakan yasa ya leka ta tagarsa, sai ya gano an janye kofar karfe da ya yi amfani da shi ya rufe inda ragon sallarsa ya ke. 

"Hakan yasa ya fito kuma ya gano ragon da ya siya N120,000 baya nan." 

Oyeyemi ya ce Abolere ya bada labarin cewa wadanda ake zargin suna kokarin tilastawa ragonsa shiga bayan mota kirar Mazda a lokacin ne ya janyo hankalin mutane. 

Post a Comment

Previous Post Next Post