Wasu Gungun Matasa Sun Lakaɗawa Wata Budurwa Duka Akan Ta Daci Generator


Yanzu yanzu muke samun labarin yadda wasu fusatattun matasa sukayi ta dukan wannan budurwar dalilin satar waya da Engine generator datayi a wurin mai chaji.

Wata budurwa mai suna Emanuella blessing ta shiga shagon wani mutum da tsakar rana a jihar Lagos dake kasar nigeria.

Inda tayi satar injin wuta na generator tare da wayar salula ta hannu dalilin neman biyan bukatar ta akan abinda zata ci tare da iyayen da kuma yan uwanta.

Emanuella ta bayyanawa manema labaran gidan jarida na Janzakitv, cewa ita ba barauniya bace talauci shine yasa ta aikata wannan abu bawai da son ran’ta ba.

Hakika Emanuella ta bayyana matsin halin da suke fama dashi na rayuwa kuma ita bazata iya wata Sana’a ba saboda bata da lokaci dalilin kuwa tace ita daliba ce.

Yanzu haka dai wasu fusatattun matasa sunyiwa wannan budurwa shegen duka tare da mikata wurin hukuma domin ta Karasa aikin ta akan wannan budurwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post