Ga Haɗin Sabuwar Amarya



Yana da kyau ga duk wata sabuwar Amarya da aka kusa auren ta san wasu abubuwa tun kafin lokaci ya kure mata.

Kowanne Mutum Namiji ko Mace yana dauke da abu 2 a jikin sa, Sanyi da kuma Basjir, wanda dama Manzon Allah S.A.W yace mafi yawan cutar da take damun Mutane sanyi ne musassasinta.

Don haka ga wasu abubuwa sa zamuyi bayani akan su domin kawar da wadannan matsalolin.

• Karin Ni’ima dauwamammiya

• Sanyi ko wanne iri

• Basir ko wanne kala

Ga wasu abubuwa da zamu lissafo su a kasa wanda za’a yi hadin maganin da su.

A sami Tafarnuwa ko yajin ta kimanin gwangwani 1, sannan sai a sami Na’a-Na’a busassiya wanda zata yi dai-dai da Tafarnuwar, sai a sami Kanun fari kamar na Naira 100, sai kuma a sami Rai dore busasshen ganye kamar cikin hannu 1, sai a sami jijiyar Zogale kamar gindi 3 manya ko kuma wanda ta Bushe.

Idan an sami wadannan abunuwan da muka lissafa sai a hade su waje daya, sannan sai a musu dakan laushi bayan a gama dakawa sai kuma a raba su gida biyu dai-dai da dai-dai.

Da farko za’a dauki rabi sai a sami Zuma wacce zata wadatar sosai sa a zuba a cikin hadin magamin, sai a garwaya su waje daya sai a rinka shan babban cokali daya da daddare.

Sannan shima daya rabin maganin sai a sami Ruwan Zam-Zam wanda zai iya, sai zuba a kwanba tare da hadin maganin a rinka shan sa da Asuba kafin aci komai kamar cokali 3, sai a cigaba da yin hakan har tsawon kwana 7.

Wannan hadin da muka kawo muku insha Allahu idai kuna amfani da shi to zaku rabu da duk wata matsala ta Sanyo ko basir, sannan zaku sami dauwamammiyar Ni’ima.

Post a Comment

Previous Post Next Post