Rajasthan, Indiya - Kanhaiya Lal, wani mutum 'dan kasar Hindu ya rasa ransa a Rajasthan da ke Indiya bisa zarginsa da goyon bayan wanda yayi batanci ga Annabi Muhammad.
A ranar Talata, wasu maza biyu da suka zo masa a matsayin kwastomomi sun kai farmaki gami da halaka Lai, wanda tela ne yayin da yake aunasu a shagonsa da ke anguwar Udaipur.
An yi bidiyon wanda lamarin ya auku dashi yayin da aka halaka shi tare da dorawa a yanar gizo. Kamar yadda BBC ta ruwaito, makasansa sun yi ikirarin cewa sun yi hakan ne don daukar fansa a kan mutumin bisa marawa maganar Nupur Sharma, wanda kakakin jam'iyyar Bharatiya Janata ta kasa ne (BJP), wacce ta janyo cece-kuce a kan Annabi Muhammad.
DUBA: Bibiyemu a HAUSACONNECT.COM don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye a shafin intanet.
An gano yadda Sharma ya yi furucin, wanda ake gani a matsayin laifi kan Annabi Muhammad yayin wata muhawara a watan Mayu. An zargi Lal da yin wata wallafa a shafin sada zumuntar zamani tare da marawa furucin Sharma.
Foreign Newspaper ta bayyana yadda aka gano biyun da ake zargi a bidiyon gami da kamasu, Haka zalika, gwamnatin Indiya ta dakatar da amfani da yanar gizo na wani lokaci tare da haramta dandazon taro.
Tags:
Labarai