Masha Allah Kalli Bidiyon Safiya Musa Tsohuwar Jarumar Kannywood A Tiktok Yadda Ta Chanja A Gidan Mijinta


Matane da dama sun cika da Mamaki ganin yadda kamannin wannan jarumar duka Suka canja wanda kowa yasan ta abaya ba haka takeba lokacin tana kannywood ta kasance mace mai karamar jiki kai kace bafulatana ce domin yadda take a baya gata fara kuma shiru shiru duk kamannunta na yan Fulani ne

Bayan ta kwashe shekaru da dama ba aji motsin taba shiru wanda mutane sunji dadin haka daman haka ake fata duk wani dan Film musamman mata idan sukayi aure a daina tunawa dasu sai anga wani tsohon Film dinsu shine ake tunawa dasu amma wasu sunayin aure bayan wani lokaci kadan sai su dawo wanan abin yana batawa mutane rai.

Kalli Bidiyon 👇👇👇 Karku Manta Ku Danna Sau 3 Zai Buɗe 👇👇👇

Ita kuwa wannan tsohuwar jarumar ta dauki a ƙalla kusan shekara goma babu wanda yaji motsinta shiru hakan ba karamin burge mutane yayi ba domin tun abaya an santa bata da hayaniya ko wani bata taɓa aikata wani abu a wannan masana’anta ba wanda zata jawowa kanta zagi ba.

Sai dai a wannan karan tazo da wani abin mamaki wanda mutane suka cika da mamakin cewa anya kuwa wannan tsohuwar jarumar kannywood ce wato safiya Musa abin ya bawa Kowa mamaki ganin yadda ta canja tayi kina bayan a baya kowa yasan ta siritiya ce amma kasancewar aure wanda tayi yasa wannan jarumar ta chanja ta zama uwa kowa birgeshi take.

Ana so ragowar jarumai wa’yanda suke yi aure kwanan nan dasu kasance kamar wannan jarumar wajen rike aure da mutunci da sanin cewa ibada suke shine zaisa aurensu yayi tasiri.

Post a Comment

Previous Post Next Post