Yadda Matata Ta Haifu Wajen Masu Garkuwa Da Mutane A Zamfara



Wani magidanci da matsarsa ta haihu a hannun ƴan bindiga ya ce babu abin da zai ce sai addu'ar Allah ya kuɓutar da ita, domin a yanzu ƙaddara kawai suka runguma.

Magidancin mai suna Kwamared Sanusi Isa, mazaunin wajen Gusau ne babban birnin jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya.

Ya ce matarsa mai juna biyu da aka sace a farkon makon nan ta haifi ‘ya mace a hannun masu garkuwa da ita.

Kwamared Sanusi Isa Gusau ya shaida wa BBC cewa matar ta haihu ne kasa da kwana daya da sace ta kuma har yanzu ita da jaririyar da ta haifa na hannu masu garkuwar da su.

Faruwar Al'amarin

Kwamared Sanusi mazaunin birnin Zamfara ya ce a daren ranar Litinin wasu mutane suka je gidansa, ya jiyo suna ta bugun kofa har suka ɓallata bayan shafe minti 30.

Kafin Allah ya ba su ikon shiga gidan sai ya yi sauri ya ɓuya a cikin banɗaki, da suka shigo gidan sai suka iske matarsa kawai mai tsohon ciki, wadda ba ta iya ɓuya ba saboda yanayin da take ciki, a cewarsa.

Wannan ya ba su sa'ar tafiya da ita, kuma ba su sake jin wani labari ba, har sai zuwa yammacin Talata da ta kira su da wayarta da aka sace ta, take sanar da cewa ta haifi ɗiya mace, in ji Sunusi.

Mijin ya ce tun sannan dai ba su sake jin komai ba, sai dai ya ce duk da cewa har yanzu babu wani labari, jami'an tsaro na iya ƙoƙarinsu domin ganin sun ceto ta.

Sannan ya ce ɓangaren masu garkuwa da ita ba su kira sun nemi wani abu ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post