Da Ɗumi Ɗumi: Kotu Ta Yanke Wa Wani Sanatan Nigeria Hukuncin Zaman Gidan Yari



Kotun Daukaka Kara da ke Jihar Legas ta yanke wa Sanata Peter Nwaoboshi hukuncin daurin shekaru 7 a gidan gyaran hali saboda almundahar kudi Baya ga daurin.

 kotun ta kuma umurci hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kwace wasu kamfanoni biyu mallakar Sanata Nwaoboshi Da farko Sanata Nwaoboshi wanda ke wakiltar Delta North ya yi nasara a Babban Kotun Tarayya kafin EFCC ta tafi kotun daukaka kara ta yi nasara.

Yanke hukuncin na zuwa ne bayan EFCC ta daukaka kara kan hukuncin da Mai shari'a Chukwuemeka Aneke na Kotun Tarayya Abuja ya yanke a ranar 18 ga watan Yuni 2021 ba wanke wanda ake zargin daga tuhumar da ake masa.

 EFCC ta gurfanar da wadanda ake zargin su uku kan zargin mallakar wani kadara mai suna Guinea House, Marine Road, Apapa Lagos kan kudi Naira Miliyan 805. 

An yi zargin cewa wani kaso cikin kudin siyan gidan, Naira miliyan 322 da Suiming Electrical Ltd ta tura a madadin Nwaoboshi da Golden Touch Construction Project Ltd kudin ne haramtacce.

 Amma, a hukuncinsa, Mai shari'a Aneke ya ce hujja ta PW "ta nuna cewa wanda aka yi ƙarar ya karbo bashin N1.2bn daga wani bankin zamani don siyan karin kayayyaki a matsayin jari. 

Post a Comment

Previous Post Next Post