Kotu: Anyi Sa'inSa Tsakanin Alƙali Da Lauyan Shiehk Abduljabbar Nasiru Kabara...

 


A zaman yau, Shehu-Usman ya roki kotu da ta bai wa wanda yake kare wa damar shigar da cewa bashi da wata tuhumar amsawa a gaban kotun.

Lauyan wanda ake kara ya caccaki tambayoyin da wadanda ke kara suke wa wanda yake karewa kuma ya yi barazanar ficewa daga kotun. 

"Akan mene masu kara zasu dinga tambayar wanda ake kara lokacin da mahaifinsa ya rasu? Baya kunshe a cikin zargin," yace. 

Tun farko, alkalin ya amincewa lauyan masu kara da ya cigaba da tambayoyinsa kuma lauyan wanda ake karewa ya tattara komatsansa tare da ficewa daga kotun.

Ya kara da bukatar a bashi kwafin takardun shari'ar inda ya kara da cewa zai kalubalanci hukuncin a kotu ta gaba.

A yayin tambayoyi, Abdullahi ya tambaya Kabara lokacin da mahaifinsa ya rasu kuma shekarunsa nawa a lokacin? "Bayan rasuwar mahaifinka, a ina ka cigaba da karatu?" Ya tambaye shi. Wanda ake kara ya sanar da kotun cewa Sheikh Dr Nasir Kabara ya rasu a 1996.

 "A lokacin ina shekaru 25 ko 26 da haihuwa kuma bayan rasuwarsa ban sake halartar wata makaranta a Najeriya ba" Alkali mai shari'a, Ibrahim Sarki Yola, yace lauyan wanda ake kara yana da damar kalubalantar zargin da ake yi wa wanda yake karewa a kowanne mataki na shari'ar.

 Rigima ta kaure tsakanin Abduljabbar Kabara da Lauyoyinsa har ta kai Alkali ya daga shari’a A wani labari na daban, jama’a sun ga abin mamaki da aka koma babban kotun shari’a da ke Kofar Kudu, garin Kano a shari’ar da ake yi da Abduljabbar Nasiru Kabara. 

Jaridar Daily Trust ta samu labari cewa shehin malamin da ake zargi da batanci da cin mutuncin Annabi (SAW) ya zargi lauyoyinsa da yin ba daidai ba. 

Kamar yadda muka samu labari, da aka koma kotu a ranar Alhamis, 16 ga watan Satumba, 2021, Haruna Magashi ya bukaci damar su daina kare malamin.

   

Post a Comment

Previous Post Next Post