Kalli Bidiyon Harin Gidan Yarin Da Ƴan Bindiga Suka Kai A Babban Birnin Nigeria, Abuja



NAN: ta ruwaito cewa an girke motocin yaki a kewayen harabar gidan yarin na Kuje, yayin da tawagar jami’an tsaro ke ta shawagi a motocin fatrol.

 Yan sandan tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro; sun killace hanyoyin da zai sada mutum da yankin gidan yarin sannan an hana zirga-zirga a yankin.

An kuma gano jiragen yan sanda suna shawagi a sama yayin da bankuna da wasu makarantu suka kasance a kulle saboda tashin hankalin da ke yankin.

Sauran jami’an tsaro ma sun kasance cikin shirin ko ta kwana domin hana duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya, rahoton Vanguard.

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewar kimanin fursunoni 600 ne suka tsere daga gidan gyara hali na Kuje biyo bayan harin da wasu yan ta’adda suka kai a yammacin ranar Talata, 5 ga watan Yuli, Channels TV ta ruwaito.

A yayin wata ziyara da ya kai cibiyar, sakataren din-din-din na ma’aikatar cikin gida, Mista Shuaibu Balgore, ya yi bayanin cewa an dawo da fursunoni sama da guda 300 kuma wasu na kan hanya. 

Ya kara da cewar cibiyar na dauke da fursunoni 994 kuma cewa maharan, wadanda yake zaton yan Boko Haramn ne sun farmaki cibiyar don kubutar da abokan harkarsu, rahoton PM News.

Post a Comment

Previous Post Next Post