Assalamu alaikum barkanku da kasance da shafin mu Hausaconnect.com, shafin dake kawo muku labarai kowacce rana.
Kamar kullum yau ma mun samu wani mummunan labarin daya faru da tsohuwar jarumar cikin shirin Fina’-finan hausa ta kannywood, wacce kukafi sanin sunan ta da jaruma zainab abdullahi indomie.
Zainab abdullahi indomie ta kasance jarumar datayi tashe cikin masana’antar ta kannywood a shekarun baya inda tayi fice sosai cikin masana’antar ta kannywood.
Dalilin daya saka jarumar Ba’ajin duriyar ta cikin finan-finan na kannywood sakamakon wata jarrabawa data sameta ta rayuwa sakamon doguwar rashin lafiya da jarumar ta gamu da ita.
Hakika dalilin wannan rashin lafiyar ne kungiyar masana’antar kannywood ta daina yayin jarumar inda ganin haka yayi sanadiyyar barin jarumar cikin masana’antar a shekarar 2014.
Yayin da jarumar ta koma izuwa wani yanki da zama kusa da babban birnin tarayyar abuja dake Nigeria, Inda take zama cikin wani Gidan gala domin samun kudin abinda zata sai magani na jinyar ta.
Jarumar ta bayyana cewa hakika bazata ta6a mantawa da jarumi Adam a zango ba, cikin masana’antar kannywood sakamakon shine mutumin daya nunamana kulawa lokacin tana cikin wannan halin da kowa ya gujeta.
Majiyar Shafin mu: Hausaconnect.com, ta rawaito cewa yanzu haka dai jarumar ta samu sauki kuma ta dawo harkar fiim karkashin kamfanin jarumi Adam a zango mai suna White House Family.
Karshen labaran kenan kada ku manta ku kasance da shafin mu Hausaconnect.com, domin samun labaran mu akowacce rana.