Bidiyon Tsohon Shugaban Ƙasa Obasanjo Yana Ɗaukar Fasinja A DaiDaita Sahu



Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya dauki fasinjoji kyauta a Adaidaita SahuPublished 1 day ago on 02/07/2022 By Tijjani Adamu.

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya tuka babur mai kafa uku, inda ya debi fasinjoji kyauta.

Obasanjo, ya bi ta wasu hanyoyi a Abeokuta, babban birnin Ogun, don daukar fasinjoji, lamarin ya dauki hankulan mutane da dama wadanda su ka yi wa tsohon Shugaban kasa murna tare da daukar hotunan sa.

Obasanjo wanda ya rinka daukae mutane kyauta a ranar Asabar, ya zarce ta Moshood Abiola, NNPC Mega Station, Kasuwar Kuto, da dai sauransu.

Aikin wani bangare ne na shirin Keke na OBJ @ 85 na Cibiyar Bunkasa Matasa na Laburaren Shugaban Kasa na Olusegun Obasanjo (OOPL).

A cikin jawabinsa, Obasanjo ya yi kira ga matasa cewa kar su bar masu tada zaune tsaye.

Tsohon shugaban ya ce, duk da kalubalen da ake fuskanta, ya kamata su yi kokarin amfani da damar da ake da su domin yin tasiri ga al’umma.

“Dole ne matasa ku dunkule ku byar da gudummawa, domin ganin abubuwa su kasance kamar yadda ya kamata.

“Idan kun bar abubuwa ga masu yi muku almundahana sun cigaba da shugabanci, komai ba zai tafi daidai ba, domin ku ne shugabannin gobe, ba za ku taba samun haka gobe ba.

“Allah ya baka ikon zama abin da ke so ka zama. Idan kuka yanke shawara, Allah zai taimake ku ya samar da mutanen da za su taimake ku,” A cewra Obasanjo.

Post a Comment

Previous Post Next Post