Sharuɗa Biyu Ga Jamɓiyun Da Keson Canja Abokan Takarar Su-- INEC


Kwamishinan yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a na INEC, Festus Okoye, ne ya bayyana hakan cikin wani shirin gidan talabijin na Channels,  a ranar Juma’a.

Jam’iyyar siyasa ba za ta iya maye gurbin wanda aka zaba ba, sai a lokuta biyu: idan wanda aka zaba ya mutu. Ko kuma idan wanda aka zaba ya janye daga takarar.

In har janyewa ce dole ne ya kasance akwai wasikar da wanda aka zaba ya rubuta wa jam’iyyar siyasa, wanda ke nuna cewa ya janye daga takarar, tare da rantsuwar rantsuwa.

Idan ba a manta ba jam’iyya mai mulki APC, ta sanar da cewar ta zabi Kabiru Ibrahim Masari a matsayin mataimakin Tinubu ma wucin gadi.

Kazalika ma jam’iyyar NNPP, ta zabi wanda zai yi Kwankwaso takarar mataimakin shugaban kasa na wucin gadi.

INEC ta bayyana sharudan ne ga jam’iyyun da ke da muradin sauya dan takara.

Post a Comment

Previous Post Next Post