Gwamnonin arewa sun bai wa al'ummar Tudun Birin gudunmawar naira miliyan 180...


Gwamnonin arewa sun bai wa al'ummar Tudun Birin gudunmawar naira miliyan 180

Kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta bayar da tallafin naira miliyan 180 ga dagin mutanen da harin Tudun Biri ya rutsa da su.

A taron da ƙungiyar ta gudanar karon farko tun bayan kafa sabuwar gwamnati

Ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahya, ta bayyana haka ne a lokacin taron da ta gabatar a gidan gwamnatin jihar Kaduna.

Gwamnonin sun kuma buƙaci a gabatar da cikakken bincike domin gano waɗanda ke da hannu a lamarin.

A farkon wannan wata ne dai wani jirgin sojin Najeriya maras matuƙi ya kai hari kan wasu fararen hula masu maulidi a ƙauyen Tudun Biri da ke ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Kalli video..
👇👇👇👇👇



Post a Comment

Previous Post Next Post