KUYI HAKURI: Nasara ga Azzalumi na karamin lokaci ne kawai kamar dai yadda Allah ya bawa Fir'aauna dama ~Cewar Khalifa Muhammadu Sanusi Lamido.
Tsohon sarkin kano Muhammadu Sanusi Lamido Na II a wani bidiyo dake yawo a kafafen sada zumintar zamani an hango shi Yana cewa Idan kana tare da Allah karka ji Tsoron wanda yace shi ba Ruwansa da Allah domin ko da yayi wata Nasara ko galaba ta dan lokaci ne Dan Kadan, kuyi hakuri za ku ga karshen al'amarin yadda zai kare watakila Allah ya bashi dama ne domin ya halaka shi, ku duba fir'auna babu Abinda Baiyi ba kafin zuwan Annabi Musa da bayan zuwansa amma Annabi Musa yace kuyi hakuri Ubangiji zai halaka makiyinku Kuma haka Allah ya yi daga karshe.
Jama'a da dama na cewa wannan furuci na Muhammadu Sanusi Lamido na da nasaba ne da dambarwar Yanke hukuncin shari'ar jihar Kano.
Ga cikakken rahoto nan mun kawo muku a kasa domin ku kalla....
Kalla....