Shin kun san yaushe ne ranar bikin jaruma Rukayya Dawayya da Isma’ila Na’abba Afakallahu


Batu akan ko yaushe ne bikin jaruma Rukayya Umar wacce aka fi sani da Rukayya Dawayya, wacce kuma ta kasance mai tsara fina-finai a masana’antar Kannywood da kuma shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Isma’il Na’abba Afakallahu dai abu ne da mutane da dama suka kosa su sani.

Maganar soyayya dai tsakanin jaruma Rukayya Dawayya da kuma Isma’il Na’abba Afakallahu ba wani sabon batu bane, inda duk wani mai bibiyar jarumar a shafinta na sada zumunta musamman ma instagram da Tiktok zai ginga ganin alamun hakan.

Jarumar ta kasance tana yawan wallafa hotunan Afakallahu, hotunan ‘yayan sa da kusan duk lamuran da suka shafe shi irin su lamuran siyasa da sauran abubuwa na yau da kullum a shafukan ta na sada zumunta.

Majiyar mu ta mujallar Fim ta bayyana cewa, batun soyayya tsakanin Rukayya Dawayya da Afakallahu abune da aka dade ana gudanar wa cikin sirri.

Sai dai da abubuwa suka kan kama ne jarumar ta fara bayyana wa duniya cewa, akwai alaka ta soyayya tsakanin ta da shugaban hukumar tace fina-finan Isma’ila Na’abba Afakallahu.

Majiyar tamu ta kara da cewa, ta samu bayanai daga majiya mai karfi kan cewa, maganar auren Rukayya Dawayya ya riga da ya matso kusa sosai.

Ana sa ran cewa, daga yanzu zuwa kowanne lokaci za’a iya daura auren, wasu da Mujallar Fim din ta tattauna dasu sun bayyana cewa akwai yiwuwar ba wani taro za’a yi ba wajen bikin.

Sai dai sun bayyana cewa, lallai sai sun yi taro sun yi shagali sabida a cewar su, Rukayya Dawayya ba karamar mace bace.

Sun kara da cewa, hadin Afakallahu da Rukayya Dawayya yayi dai-dai sosai inda suka kara da cewa, da zarar sun kammala shirye-shiryen da suke kai a yanzu zasu bayyana ma jama’a koyau she daurin auren ba tare da wani bata lokaci ba.

A kwanakin baya-bayan nan ne dai akaga jarumar ta matsa kaimi wajen wallafa hotuna da kuma abubuwan da suka jibanci masoyin nata a shafukan sada zumunta musamman ma Tiktok da instagram.


Post a Comment

Previous Post Next Post