Maza ba mutanen kirki ba ne, ku ƙaurace musu – Safara’u Kwana Casa’in


Matashiyar mawakiyar nan a arewacin Najeriya, Safeeya Yusuf, wadda aka fi sani da Safara’u Kwana Casa’in, ta bayyana cewa Maza ba mutanen kirki bane dan haka a ƙaurace musu.

Safara’u Kwana Casa’in ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter a jiya Talata, inda mabiyan ta a shafin ke cigaba da tafka muhawara akan furucin na ta.

SANARWA!!!
Ga Bidiyon 👇👇👇👇 Karku Manta Ku Danna Sau 3 Zai Buɗe...



“Maza ba mutanen kirki ba ne! Dan haka a ƙaurace musu.” In ji Safara’u

Safara’u Yusuf dai tsohuwar jaruma ce da ta ke fitowa a cikin shirin Kwana Casa’in da Arewa24 ke shiryawa, kafin masu shirya fim din sun dakatar da ita daga shirin sakamakon yadda wani bidiyon tsiraicinta ya karade shafukan intanet.

Haka kuma al’umma na ganin waƙoƙin da Safara’un ta ke yi a yanzu suna ɓata tarbiyya, ko da yake ta ce tana fadakar da jama’a ne.

Post a Comment

Previous Post Next Post