Innalillahi Wa'inna Ilaihin Rajiun -Yadda wani matashi ya halaka ƙanin sa wajen gwada maganin bindiga


Wani abin jimami ya auku a jihar Kwara inda wani matashi ya halaka ƙanin sa yayin gwada maganin bindiga.

Matashin mai suna Abubakar Abubakar ya harbi ƙanin sa har lahira mai suna Yusuf Abubakar ɗan shekara 12, domin gwada ingancin sabon maganin bindigan da suka siyo. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Mahaifin yaran yana da bindigar farauta
Abubakar mamacin ƴaƴan wani mafarauci ne a ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar Kwara.

An samo cewa lamarin ya auku ne a ranar Lahadi, sannan matashin Abubakar yayi ɓatan dabo tun bayan aukuwar lamarin. Ya gudu ne bayan ya aikata wannan ɗanyen aikin.

Hukumomi sun tabbatar da aukuwar lamarin
Da yake magana kan lamarin a ranar Litinin, kakakin hukumar ƴan sandan jihar Kwara, Okasanmi Ajayi, yace kwamishinan ƴan sandan jihar Paul Odama, ya bayar da umurnin a gudanar da bincike.


Post a Comment

Previous Post Next Post