Harkar Film tayi mun komai a rayuwata – Inji Karima Izzar so


Jaruma Khadija Yobe wacce aka fi sani da Karima Izzar so wacce fitacciyar jaruma ce a masana’antar fina-finai ta Kannywood ta bayyana cewa Film yayi mata komai a duniya nan domin kuwa da shi take ci take sha take gudanar da hidindimunta harma ta taimaki waɗansu, yayi mata riga da wando.

Jarumar ta bayyana hakan ne a hirar ta da sashin Hausa na BBC a cikin wannan fitaccen shirin nasu na Daga bakin mai ita, wanda yake tattaunawa da wasu shahararrun mutane inda suke bada labarin irin gwagwarmayar da suka sha a rayuwarsu.

Karima Izzar so dai tayi fice ne tunda ta fara fitowa a cikin fitaccen shirin nan mai dogon zango wato Izzar so. Jarumar tayi fina-finai da dama kama daga na bai ɗaya zuwa ga masu dogon zango waɗanda har yanzu ana cigaba da yin wasu daga ciki. Sai dai babu inda jarumar tafi yin suna fiye da Izzar so.

Yadda Karima Izzar so ta shiga harkar Film
Da aka tambaye ta ko ta yaya ta tsinci kanta a cikin masana’antar Kannywood, Karima Izzar so ta bayyana cewa tun tana yarinya ‘yan film suke burgeta. Bayan data girma, jarumar tace tana tasowa daga Yobe tazo Kano don kallon sabon film idan za’a haska shi a cinema. Ta ƙara da cewa tana son ‘yan film sosai a ranta.

Ta bayyana cewa ta shiga harkar film ne ta hanyar yayanta da kuma wani abokin shi. Ta fara da shirin film din Izzar so wanda ta bayyana cewa ya zame mata bakandamiya wanda kuma take kyautata zaton zai amfaneta tun daga nan duniya har zuwa lahira.

Izzar so ya zame mun bakandamiya a rayuwata
“Gaskiya wannan fim ya kasance mun bakandamiya a rayuwa ta, wanda zai amfane ni daga nan duniya har zuwa lahira. Haka nake zato, in sha Allahu kuma haka ne zai kasance saboda film ne da yake faɗakar da al’umma na hanyar gaskiya da amana, da kuma koyi da manzon Allah (S.A.W).” inji jaruma Karima Izzar so.

Karima Izzar so ta ƙara da cewa tayi fina-finai da dama fiye da yadda ba’a tunani, kuma a yanzu haka ma tana tana kan yin wasu. Jarumar ta ƙara da cewa tana jin ɗaɗin aiki da duk jarumin da aka haɗa ta dashi ma damar mai kuzari ne da nuna jajircewa a yayin gudanar da aikin.

Jarumar ta ƙara da cewa tana zaman lafiya da duk abokanan aikin ta kuma suna ƙaunar junan su kamar ‘yan uwan juna. Ta bayyana cewa yanzu haka suna da gidauniya ta Izzar so wacce suke amfani da ita wajen taimakawa masu buƙatar taimako daga cikin su.

Bazan taɓa mancewa da mutuwar Nura Mustapha ba
Karima ta bayyana cewa mutuwar darakta Nura Mustapha Waye ta dugunzuma ta sosai, bazata taɓa mancewa da ita ba.

Jarumar ta ƙara da cewa tana zaman lafiya da duk abokanan aikin ta kuma suna ƙaunar junan su kamar ‘yan uwan juna. Ta bayyana cewa yanzu haka suna da gidauniya ta Izzar so wacce suke amfani da ita wajen taimakawa masu buƙatar taimako daga cikin su.

Bazan taɓa mancewa da mutuwar Nura Mustapha ba
Karima ta bayyana cewa mutuwar darakta Nura Mustapha Waye ta dugunzuma ta sosai, bazata taɓa mancewa da ita ba.


Post a Comment

Previous Post Next Post