Wannan shine Ya'u Abdullahi, Ma'aikacin Lantarki (KEDCO) da wuta tajashi jiya a Civic Center dake jihar Kano wurin kokarin ceton mutanen da gini ya danne, ya kuma koma ga Mahalaccin mu.
Wannan bawan Allah ya cancanci girmamawa da kuma addu'a domin samun irinsa a wannan zamanin abune mai matukar wahala sanadiyyar Ceton wasu mutane ya rasa ransa Allahu Akbar.
Al'umma da dama sai fatan rahamar Allah sukeyi a gare shi, dashi da wayan da gini ya danne baki daya Allah ya gafarta masu.
Muna addu'ar Allah yaji Kansa da Rahma.
Tags:
LABARI