Innalillahi: wani Ragon layya ya kucce ya yi dare-dare akan kwano
Wani gudajjen rago ya kufce a safiyan yau daidai lokacin da ake yunkurin masa kisan gilla a matsayin ibadar layya.
Layya dai sunnan Manzon Allah ne mai karfi wanda dukkan musulmin duniya suke aikatawa ka’in da na’in.
Ya tabbata a hadisin Annabi cewar duk wanda yayi layya yana da dalan kwatankwacin kowane silin gashin da ke jikin dabban da ya yanka.
Hakika samari da dama suna gudun wannan aikin lada, domin kuwa sun mayar da wannan yanka na laiya tamkar masu mata ne kadai aka umurta da suyi.
Sai dai kuma a wayewar garin yau dinnan ne wani kasurgumin rago ya balle yayi wuf ya haye saman kwanon gidan makota, kuma anyi-anyi ya sauko amma yayk kemadagas ya ki saukowa.
An dai ji mai wannan ragon yana kwalla ihun neman taimakon jama’a ne akan al’umma su dubi Allah su agaza masa wajen ganin an sauko da wannan gudajjen ragon nasa domin ya samu ya gabatar da wannan ibada ta layya.
ArewaTimes Hausa ta binciki yadda abin ya samo asali, sai ta gano cewar mai ragonne yayi sakaci, kana kuma ya firgita shi ragon, domin kuwa ya bari ya ji labarin abinda za a yi da shi, bugu-da-kari ya bari ya jiyo kamshin suya a makota.
Tags:
Labarai