Wata mata a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta haifi jarirai hudu rigis a lokaci daya, wadanda dukkanninsu mata ne, a babban asibitin Shinkafi.
A bayanin da daya daga cikin ma’ikatan asibitin da suka karbi haihuwar, ungozoma Hajiya Kulu ta yi wa BBC ta ce, tun da farko hoton cikin da aka dauka ya nuna cewa matar na dauke da jarirai uku ne.
Amma kuma bayn da ta haifi ukun sai aka ga cewa akwai alamun karin na hudu, wanda shi ma ta haife shi.
Jami’ar ta ce dukkanin jariran da mahaifiyar tasu suna nan cikin koshin lafiya, amma kuma ta ce akwai matsalar da ake fuskanta, saboda ya kamata a sa su cikin kwalba amma kuma asibitin ba shi da wannan na’ura.
Hakan dai ya kasance wani kaluble a garesu domin iyayen masu karamin karfi ne, in ji ungozomar.
Mahaifin jariran, Mallam Is’haqa Isa, ya bayyana wa BBC cewa yana godiya ga Allah da Ya azurta shi da wadannan yara.
Amma kuma ya ce yana neman taimako daga jama’a kasancewar ba shi da ko naira dubu biyar a halin yanzu, hasali ma ba shi da aikin yi, sannan kuma gurgu ne shi.