Alhamdulillah!! Allah Ya Azurta Mawaki Garzali Miji Da Samun Haifuwar Ɗa Namiji.


Kamar yadda kuka sani da a watannin baya da suka gabata anyi auren jarumi kuma mawaki a masana’antar shirya fina-fina hausa ta kannywood Garzali Miko.

To sai kuma a jiya wallafa wani hoton jariri a shafin sa na sada zumunta instagram yana mai cewa, Allahamdullah Allah ya Azurtani da Da namiji yau, 7/06/2022 Allah Abin Godiya Allah yasa Kazo Duniya A sa’a ,Allah ya Amfani Rayiwarka.

Hakan ya nuna mana cewa, Garzali Miko ya sami karuwa ta haihuwar Da Namiji, muna rokon Allah ya albarkace shi ya raya shi kan sunnar Annabi Muhammad S.A.W.

Kalli Hotunan A Ƙasa:👇👇👇







Post a Comment

Previous Post Next Post