Ahmad Musa Ya Caccaki Gwamnati Akan Yakin Aikin Assu


Kuna kai Ziyara Makarantun Yayanku a Kasashen Waje Har kudauki hoto, bayan Su kuma Yayan Talakawa nan a gida Kun rufe nasu Makarantun – Martanin Ahmed Musa ga Gwamnatin Nigeria.

Fitaccen dan kwallon kafar Najeriya, Ahmed Musa ya caccaki masu rike da mukaman siyasa a Najeriya kan yajin aikin da malamai ke yi a kasar.


Ahmed Musa yayi wannan korafi ne a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram, inda yake tambayarsu irin yanayin yadda suke ji idan sun ziyarci yayansu a kasashen waje kuma su ringa daukar hotuna tare dasu a makarantunsu suna wallafawa a Shafukan su na sada Zumunta a yayin da su kuma yayan talakawa suna gida yajin aiki ya hanasu komawa.

Ahmed Musa ya kara da cewa su kansu shuwagabannin siyasar Nigeria basu yarda da tsarin da suke gudanar ayyukan suba wanda hakan yama zama abin kunya kenan.

Ahmed musa dai wanda a wallafar da yayi alamu sun nuna cewa ranshi ya baci akan yajin aikinda ASUU sukeyi kasancewar a yanzu kusan wata na hudu kenan ake ciki kuma yayan talakawa suna gida zaune babu alamun komawa.



Post a Comment

Previous Post Next Post