Wata rana wani ustazu ya je shagon mai sayar da finafinan batsa. Ya sha hirami ga dan gemu kamar tsohon bunsuru. Ya na isa ya ce, “salamu alaikum wa rahmatu Allahi ta’ala wa barakatihu”. Su ka ansa, ” wa alaikum mussalamu ya ustazu.” Ya ce, “ya ‘yan’uwa wato ainihin nan ne ake sayar da finafinan batsa?” Su ka ce, “na’am nan ne ya ustazu.” Ya ce, “Subhanallah Allah shirye ku, a nawa nawa ku ke sayarwa?” Su ka ce, “dari uku ya ustazu.”
Ya daga gemu sama, “wa iyazu billah, kayan banza sai tsada. To a kawo min su in gani.” Su ka mika mai, “ga su ya ustazu”, ya duba ya kau da kai ,”inna li Allahi wa inna ilaihi raji’un, a sa min guda uku a bakar leda in je ni gida in ta la’antar su ga kudin ku.” Su ka mika mai ya ce, “na bar ku lafiya tsinannu Allah shirye ku. Ni kuma zan je inta ma'anar su.