Yayin da babban zaben Najeriya yake karatowa, 'yan siyasa da jam'iyyu daban-daban suna ci gaba da daura damarar yadda za su karbu a wajen masu kada kuri'a.
Tun kafin hukumar zaben kasar, INEC, ta fitar da jadawalin zabukan shekarar 2023, 'yan siyasa suka soma kamun-kafa da gagganawa da zummar samun magoya baya a siyasance domin tunkarar zabukan da ke tafe.
Tuni dai shugabannin da ke kan mulki (wadanda tsarin mulkin Najeriya ya ba su damar sake tsayawa takara) da tsoffin 'yan siyasa da ma sabbin-shiga suka soma gudanar da taruka da tattanawa da masu ruwa da tsaki da abokan harkokinsu na siyasa, da ma 'yan wasu jam'iyyu a yunkurin samun nasara a zabuka masu zuwa.
Sai dai wasu daga cikin mutanen da suka ja hankalin 'yan kasar a wannan fafutika su ne 'ya'yan gwamnoni da wasu manyan 'yan siyasa da su ma suka yunkuro domin tsayawa takara a zabukan 2013.
Wasu daga cikin 'ya'yan gwamnoni da aka ga fastocinsu na tsayawa takara sun hada da Bello Elrufai, dan gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasir Elrufai da ke neman takarar dan majalisar dokokin tarayya a jam'iyyar APC.
Akwai Mustapha Sule Lamido, dan tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, da ke son tsayawa takarar gwamna jihar tasu duk da a baya yayin wata hira da BBC, Sule Lamido ya ce ba laifi bane idan ya goyi bayan ɗansa ya tsaya takara inda ya ce duk wani mahaifi yana son ɗansa.
Sannan da Abba Ahmad Sani Yariman Bakura, dan tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura, shi ma yana son tsayawa takarar dan takarar majalisar tarayya .