Yanzu Yanzu Limamin Masallacin Quba A Madina Sheikh Muhammad Abid Al-Sindi Ya Rasu


 Limamin Masallacin Quba da ke Madina, Sheikh Muhammad Abid Al-Sindi ya rasu.

A baya ya kasance yana jagorantar Sallar tarawih ne a Masallacin Annabi kafin ya koma na Quba.

Shafin Twitter na Haramain Sharifain ne ya wallafa labarin rasuwar Sheikh Al-Sindi, inda ya kara da cewa tuni an yi jana'izarsa an kuma rufe shi a makabartar Baqee da ke garin Madinah.


Haramain Sharifain ya jajanta wa al'ummar musulmai na rashin babban limamin garin Madina.

Allah Ya gafarta masa....

Post a Comment

Previous Post Next Post