An saka ranar daurin Auren Afakallah da jaruma Rukayya Umar Dawayya


Tsawon lokaci da aka shafe anata jita-jitar batun auren shugaban hukumar tace finafinai reshen jihar Kano Malam Isma'il Na'abba Afakalla da jaruma Rukayya Umar da akafi sani da Dawayya yazo ƙarshe domin kuwa an saka ranar daurin auren.

Kalli Wannan Bidiyon 👇👇👇👇

Ismail Na'abba Afakalla shine wanda ya wallafa katin gayyatar daurin auren a shafinsa na Instagram wanda za'a yi a ranar juma'a mai zuwa. Kuma Za a ɗaura auren ne da ƙarfe 2:00 na rana a ranar Juma’a, 4 ga Nuwamba, 2022 a Masallacin Juma’a na Tishama, dake Kano.

Post a Comment

Previous Post Next Post