Video Malam Bello Yabo Da Yayi Wani Zazzafan Furuci Ga Jaruman Kannywood Bayan Sakin Waƙar "Chass"

 

Shahararren malamin addinin Muslunci na nan kasa Nigeria mai suna Bello yabo yayi wani babban martani akan wasu jaruman kannywood wanda suke hawa wakokin mawaki ado gwanja da chass da kuma warr saboda yadda ake fitsara akan wa’yannan wakokin.

Malamin yace duk wacce akaga tana hawa wannan wakar kuma tana rawa ta rashin mutunci to hakika wannan mutuniyar banza ce bata da tarbiyya kuma yakamata asa jami’an tsoro su kamata.

Sannan malamin ya kara kira ga hukuma cewa indai har tana kishin tarbiyar yaya Musulmi mata to ya kamata a dauki mataki akan wannan abubuwan da jatumai mata na kannywood suke yi.

Sai ance daman wannan malamin baya rabo da zagi da kuma suka akan yan kannywood kai harda ma sauran malamai yan uwansa bai barsuba dan babu wani malami daya bari balle yan film.

Sai dai kuma na ganin kokarin malamin ganin yadda ya fadi gaskiya akan wannan abu domin duk wani me kishin yayansa to zaiyi fada da wannan abun daya fito na wakar chass.

Post a Comment

Previous Post Next Post