Innalillahi!! Asirin Wani Malami Mai Lalata Da Matan Aure Kafin Ya Basu Magani Ya Tonu



Mun samu labarin dubun wani ya cika bayan kwashe shekaru da yayi yana lalata da matan aure akan zai basu maganin mallakar miji.

A yau mun samu rahoton wani dattijo yana yaudarar mata da sunan ba su sirrin mallakar miji. Ya kasance yana lalata da su, kuma a kwanakin nan asirinsa ya tonu.

Mun samu wannan rahoto daga DCP Abdullahi Kiyawa, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, wanda shi ma ya ce an kama shi ne saboda wata yarinya da ta nemi taimakonsa.

Ya yi lalata da ita daga baya yarinyar ta kai kararsa ga ’yan sanda kuma ta bayyana abin da ya yi mata.

Bayan samun wannan bayanin ba su yi kasa a gwiwa ba suka kai wannan yarinya domin nuna musu kauyen da yake zaune da kuma gidansa. sun yi nasarar kama shi har ma sun yi masa faifan bidiyo suna neman ya bayyana wa kansa wannan mugunyar laifin da ya aikata.

Post a Comment

Previous Post Next Post